IQNA

13:05 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981700

Cibiyar Addinai Ta Duniya Ta Yi Suka Kan Ayyana Ranar Kone Kur'ani

Bangaren kasa da kasa; Cibiyar harkokin addinai ta duniya ta yi kakkausar suka dangane da ayyna ranar 11 ga watan satumba ta zama ranar kone kur'ani mai tsarki da wata majami'a ta yi a kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar sharq al-ausat cewa, cibiyar harkokin addinai ta duniya ta yi kakkausar suka dangane da ayyna ranar 11 ga watan satumba ta zama ranar kone kur'ani mai tsarki da wata majami'a ta yi a kasar Amurka domin yin izgili ga addinin Musulunci da musulmi.

A cikin wani bayani da cibiyar ta fitar a babban ofishinta da ke birnin New York na kasar Amurka ta bayyana cewa, wannan mataki da majami'ar ta dauka ya yi hannun riga da koyarwa ta kowane addini, kuma duk wani gigin yin hakan zai zama babban kuskure da majami'ar za ta tafka.

Cibiyar dai ita ce mafi girma a duniya da ta hada dukkanin addinai, kuma tana da babban tasiri wajen fada a ji a cikin harkoki da daman a kasa, kamar yadda take taka rawa wajen warware da dama daga cikin matsalolin zamantakewa.

Yanzu haka wasu daga cikin limaman majami'oin Amurka sun nuna rashin amincewarsu da matakin da masu tsanain gaba da addinin Musulunci ke son dauka na kone kur'ani mai tsarki.

641195



captcha