IQNA

Baje Kolin Kayan Tarihin Musulunci A Jami'ar Savana A Amurka

13:33 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981708
Bangaren kasa da kasa; An bude wani baje kolin kayan tarihin Musulunci a jami'ar Savana da ke cikin jahar Georgia a kasar Amurka a shekaran jiya Talata.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WSAV an bayyana cewa, a shekaran jiya Talata an bude wani baje kolin kayan tarihin Musulunci a jami'ar Savana da ke cikin jahar Georgia a kasar Amurka.

Bayanin ya kara da cewa wannan baje koli yana samun halar cibiyoyin Musulunci da ke cikin jahar, inda suke nuna wasu daga cikin ababe na tarihin Musulunci, da suka hada da hotuna na wurare masu tsarki, da kuma wasu kayyakin dadaddiyar fasahar Musulunci.

Babbar manufar gudanar da baje kolin dai ita ce wayar da kan Amurkawa dangane da tarihin addinin Musulunci, da kuma kawar da mummunar fahimtar da wasu daga cikinsu suke da ita kan Musulunci.

641432




captcha