IQNA

Jami'ar Musulunci Ta Farko A Amurka Ta Fara Ayyukanta

15:38 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981749
Bangaren kasa da kasa; Jami'ar Musulunci ta farko a kasar Amurka ta fara gudanar da ayyukanta a shekaran jiya talata a birnin Brocly na jahar California a kasar Amurka.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBS cewa, Jami'ar Musulunci ta farko a kasar Amurka ta fara gudanar da ayyukanta a shekaran jiya talata a birnin Brocly na jahar California da ke yamma maso kudancin kasar.

An bude ajujuwan farko na wannan jami'a ne da aka baiwa suna zaitunah tare da dalibai goma sha biyar a matsayin fari, daga bisani kuma za a ci gaba da daukar dalibai da ked a sha'awar yin karatu a wannan jami'a a rassa ilmomi da za a rika koyarwa a cikinta.

Daga cikin rassan da aka fara koyarwa dai ya zuwa yanzu akwai ilimin sanin ubangiji, kyawawan dabi'u na Musulunci, tattalin arzikin Musulunci.

641530




captcha