Kamfanin dilalncin lanaran iqna ya habarta cewa, babban malamin addinin Musulunci Allamah Sheikh Muhammad Jawad Balaghi ya bayyana cewa, babban hadarin da ke fuskantar al'aummar musulmi a halin yanzu shi ne kokarin shafe hawiyar Musulunci ga mabiya addinin Musulunci a cikin kasashen musulmi da sauran kasashen duniya.
Malamin ya ci gaba da cewa kasashen yammacin turai suna hankoron ganin cewa an shafe tunanin Musulunci a cikin kwakwalen al'ummomin musulmi, musamman ga matasa masu tasowa da ga cikin musulmi, ta yadda za a manta da tunanin addinin a nan gaba.
Ya ce wannan babban hadari ne ga al'ummar musulmi, kuma wajibi ne da ya rataya kansu a matsayi na al'umma ko matsayi na daidaiku, da su mike su kalubalanci wannan mummunar aniya.
641606