Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da wani baje kolin kur'ani mai tsarki da ya kebanci wasu daga cikin surorin kur'ani a kasar Malazia, tare da halartar cibiyoyin ilimi na kasar, musamman ma daga jami'oi.
Bayanin ya kara da cewa ana gudanar da wannan baje koli ne a jami'ar kasa da kasa ta birnin Kualalampour, kuma tuni aka kawo wasu daga cikin kayayyakin da ake baje kolinsu a wurin daga kasashen musulmi daban-daban.
Gudanar da wannan baje koli na da dangantaka ne da watan Ramadan mai alfarma, kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara, amma a wannan karon baje kolin ya fi bunkasa fiye da sauran lokuta.
642976