IQNA

Birnin Alkahira Ne Zai Karbi Bakuncin Taron Tattaunawa Tsakanin musulmi Da Kiristoci

13:55 - August 29, 2010
Lambar Labari: 1983492
Bangaren kasa da kasa; a karo na uku taron hadin guiwa tsakanin jami'o'in Musulunci da jami'a mai zaman kanta na Amsardam na kasar Holand na musulmi da kiristoci na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara za a gudanar da shi ne a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar.
Kafanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; a karo na uku taron hadin guiwa tsakanin jami'o'in Musulunci da jami'a mai zaman kanta na Amsardam na kasar Holand na musulmi da kiristoci na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara za a gudanar da shi ne a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar. A wajen wannan taro masana musulmi da kiristoci kimanin dari daya ne daga kasashe daban daban na duniya za su halartar.A gurin wannan taro musulmi da kiristoci za su yi nazari da bincike kan irin matsalolin da suke fama da su da kuma hanyoyin da za su bi wajen magance su ko kuma tunkararsu.

643167
captcha