IQNA

Fara Gudanar Da Mataki Na Uku Na Koyar Da Kur'ani Ta Tarho A Qatar

9:43 - August 31, 2010
Lambar Labari: 1984723
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da mataki na uku na koyar da karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar wayar tarho a kasar Qatar, wanda ya kebanci mata a karkashin shirin cibiyar bunkasa ilmomin addini tsakanin matan kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na jaridar kasar ta al-raya cewa, za a fara gudanar da mataki na uku na koyar da karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar wayar tarho a kasar Qatar, wanda ya kebanci mata a karkashin shirin cibiyar bunkasa ilmomin addini tsakanin matan kasar raf.

Shugaban cibiyar kula da ayyuakn bunkasa al'adu da harkokin ilmi a kasar ta Qatar sheikh Sani bin Abdullah ya bayyana cewa, an riga an gudanar da mataki na farko da na biyu an wannan shiri cikin nasara.

Ya ce yanzu kuma sun kammala dukkanin shirye-shiryen d suka kamata domin fara mataki na uku, wanda shi ma a cewarsa da yardar Allah za su samu nasara wajen gudanar da shi.

645006


captcha