Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Al-ittihad an bayyana cewa, Mahukuntan daular Sharja a kasar haddadiyar daular larabawa na da shirin ginawa tare da yin gyare-gyare a masallatai a kasashen musulmi marassa galihu a cikin wani shiri na watan Ramadan mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa an kaddamar da wannan shiri ga majalisar birnin Sharjah kuma tuni shirin ya samu karbuwa daga dukkanin mambobin majalisar, inda ake jiran a amince da shi domin fara aiwatar da shi.
Daga cikin muhimman abubuwan da shirin zai mayar da hanakali kansu akwai batun gina masallati a kasashen musulmi marassa galihu tare da gyara su gami da cibiyoyin Musulunci.
647086