IQNA

Wasannin Na'ura Mai Kwakwawa Na Kiyayya Da Musulunci A Austria

13:31 - September 04, 2010
Lambar Labari: 1986976
Bangaren kasa da kasa; Jam'iyar nan mai tsananin gaba da addinin Musulunci a kasar Austria ta FPO ta samar da wasu wasannin na'ura mai kwakwalwa na nuna kiyayya ga Musulunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar zaman ta kasar Turkiya an habarta cewa, jam'iyar nan mai tsananin gaba da addinin Musulunci a kasar Austria ta FPO ta samar da wasu wasannin na'ura mai kwakwalwa na nuna kiyayya ga Musulunci da ake nufin sanya su a kasuwa.

Rahoton ya ce a cikin wasanin an nuna abubuwa da dama da suke nuna matukar kyama da cin zarafi ga addinin Musulunci, tare da nuna musulmi a matsayin wasu mutane da suka yi kama da dabbobin daji marassa kan gado da rashin tausayi.

Wannan jam'iya dai ta shahara a kasar wajen nuna gaba da addinin Musulunci, a kwanatin baya ta dauki matakin kalubalantar gina masallatai a kasar.

647019



captcha