IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar Ranar Qods Ta Duniya A Baku

13:31 - September 05, 2010
Lambar Labari: 1987912
Bangaren siyasa da zamantakewa; An gudanar da jerin gwano na ranar Qods ta duniya a birnin Baku na kasar Azarbaijan a ranar Juma'ar da ta gabata taron da ya samu halartar dubban mutane.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da bangaren yada labaransa na kasar Azarbaijan ya bayar, an bayyana cewa an gudanar da jerin gwano na ranar Qods ta duniya a birnin Baku na kasar Azarbaijan a ranar Juma'ar da ta gabata taron da ya samu halartar dubban mutane mazauna birnin.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro an gudanar da shi ne a yankin Nardan da ke cikin birnin fadar mulkin kasar Azarbaijan, inda dubban mutane suka fito kan manyan titunan yankin suna gudanar da jerin gwano.

A lokacin gudanar da jerin gwanon na ranar Qods ta duniya, masu zanga-zangar sun yi tar era taken la'anta ga Isra'ila, tare da yin kira zuwa ga hadin kai tsakanin dukkanin musulmi na duniya.

647633




captcha