Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi Allawadai da fitar da wasu wasannain batunci da tozarci ga addinin muslunci da wasu masu tsananin gaba da Musulunci a kasar Austria suka yi da nufin kara yawan kyamar musulmi a kasar.
Jam'iyar nan ta masu tsattsuran ra'ayin kiristanci da gaba da addinin Musulunci ta kasar Austria ita ce ta dauki nauyin shirya wadannan wasannai na batunci ga addinin Musulunci, domin yin amfani da hakan wajen samun kuri'un duk wasu kiyayya da Musulunci a kasar a lokutan zabuka masu zuwa.
648365