IQNA

10:46 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989319
Bangaren kasa da kasa; Wakilin kasar hadaddiyar daular larabawa a gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a kasar Tusia Abdullah Abdulaziz Al-naghbi shi ne ya zo na biyu a bangaren harda.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Darul khalij an bayyan a cewa, wakilin kasar hadaddiyar daular larabawa a gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a kasar Tunisia Abdullah Abdulaziz Al-naghbi shi ne ya zo na biyu a bangaren hardar kur'ani.

Bayanin ya ci gaba da cewa mahardacin wanda ya gudanar da harda a bangaren juzu'i na goma sha biyar ya samu amincewar dukkanin alkalan gasar, inda suka tabbatar da shi a matsayi nabiyu.

Kasar hadaddiyar daular larabawa na daga cikin kasashen musulmi da suke taka gagarumar rawa wajen shiga gasar kur'ani da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa.

649366


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: