IQNA

Limamin Kirista Carnil Jan Na Taya Musulmi Murnar Eid Fetr

13:22 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990477
Bangaren kasa da kasa; Shugaban kwamitin tattaunawar addinai na duniya ya isar da sakon taya murna ga dukkanin musulmin duniya kan shirye-shiryen idin karamar sallah da za su gudanar a ko'ina cikin fadin duniya.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, shugaban kwamitin tattaunawar addinai na duniya ya isar da sakon taya murna ga dukkanin musulmin duniya kan shirye-shiryen idin karamar sallah da za su gudanar a ko'ina cikin fadin duniya baki daya.

Shugaba kwamitin tattaunawa addininai na duniya Carnil Jan ya bayyana cewa wannan lokaci na azumin watan Ramadan lokaci mai tsarki, domin kuwa a cikinsa ne musulmi suke gudanar da ibadar azumi da nufin samun kusanci da Allah.

Ya ce bayan samun kusanci da Allah da azumin watan Ramadan da musulmi suka yi, kuma za su gudanar da eid fitr, wanda shi ma rana mai albarka ta kammala ibadar azumi, a kan haka yana taya dukkanin musulmi murna.

650159




captcha