Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya kanao daga kamfanin dillancin labaran AFP an bayyana cewa, ministan Shri'a a kasar Amurka ya yi Allawadai da ayyana ranar kone kur'ani mai tsarki ta da wata majami'ar kasar ta yi, inda ya bayyana hakan da cewa babban wawacin ne kuma yana tattare da babban hadari.
Bayanin ya ci gaba da cewa ministan ya bayyana ayyana ranar kone kur'anin da cewa yin hakan zai jefa Amurka cikin wani mawuyacin hali na tashin hankali da rashin zaman lafiya, a kan haka ya zama wajibi wannan majami'a ta dawo daga rakiyar wannan tunani.
A nasa bangaren kuwa kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa 'yancin fadin albarkacin baki da bayyana ra'ayi hakkin kowa ne a Amurka, amma abin da majami'ar Folorida take son yi zai jefa Amurka cikin hadari.
651363