Bangaren kasa da kasa; Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa kone kur'ani mai tsarki ya saba wa siyasar kasarsa, kuma hakan babu abin da zai haifar illa cutar da kasar Amurka da kuma al'ummarta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar yaum sabi ta kasar Masar an habarta cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa kone kur'ani mai tsarki ya saba wa siyasar kasarsa, kuma hakan babu abin da zai haifar illa cutar da kasar Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar ta Amurka ya fito karara ya nuna rashin amincewarsa da abin da limamin kirista na wata karamar majami'ar mai mabiya 'yan tsiraru ked a aniyar yin a kone kur'ani mai tsarki a ranar 11 ga watan satumba.
Obama ya ce ya kamata Amurkawa sun kwana da sanin cewa su ba makiyan Musulunci ba ne, kuma musulmi ba makiyansu ba ne, kungiyar alka'ida ita ce babbar makiyarsu.
652323