IQNA

An Gudanar Da Taron Bankwana Da Watan Ramadan

16:10 - September 12, 2010
Lambar Labari: 1992048
Bangaren kur'ani; An gudanar da wani zaman taron karatun kur'ani mai tsarki na bankwana da watan a daren karshe na watan Ramadan a birnin Tabriz da ke jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da halartar wasu makaranta na kasa da kasa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na lardin Azarbaijan ta gabas ya habarta cewa, An gudanar da wani zaman taron karatun kur'ani mai tsarki na bankwana da watan a daren karshe na watan Ramadan a birnin Tabriz da ke jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da halartar wasu makaranta na kasa da kasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro an shirya shi domin gudanar da karatun kur'ani da nufin yin bankwana da watan Ramadan mai alfarama, watan da aka safkar da kur'ani mai tsarki a cikinsa.

Da dama daga cikin fitattun makaranta kur'ani na kasar da suke halartar gasa ta kasa da kasa sun halartci wannan taro, inda suka gabatar da karatun kur'ani.

652283

captcha