Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren huda da jama'a a bangaren bunkasa harkokin al'adu na Iran cewa, an gudanar da tarukan idin karamar salla a kasar Rasha, wanda ofishin cibiyar kula da harkokin al'adu na kasar Iran da ke birnin Moscow ya dauki nauyin shiryawa da kuma gudanarwa a birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya samu halartar musulmi daga sassa daban-daban na birnin, da suka hada da Iraniyawa mazauna kasar rasha da kuma musulmin kasar da aka aikewa da goron gayyata.
652437