IQNA

Zanga-Zangar Kare Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Afghanistan

12:19 - September 14, 2010
Lambar Labari: 1993540
Bangaren kasa da kasa; Dubban musulmin kasar Afghanistan ne suka gudanar da zanga-zangar kare kur'ani mai tsarki a sassa daban-daban na kasar Afghanistan, da wasu daga cikin tsirarun kiristocin kasar Amurka suka yi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na cri an bayyana cewa, dubban musulmin kasar Afghanistan ne suka gudanar da zanga-zangar kare kur'ani mai tsarki a sassa daban-daban na kasar Afghanistan, da wasu daga cikin tsirarun kiristocin kasar Amurka suka yi da nufin tsokanar musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka gudanar da zanga-zangar sun yi ta la'antar mutumin day a fara yin kira zuwa ga kone kur'ani a ranar tunawa da hare-haren 11 ga watan satumba.

Wasu daga cikin tsirarun kiristoci masu tsananin gaba da addinin Musulunci sun kone kur'ani tare da keta shi a gaban fadar white house a kasar Amurka.


653537
captcha