Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz na kamfanin dillanicn labaran AFP cewa, babban daraktan kungiyar hadin kasashen musulmi ta OIC Ihsan Auglo ya kirayi dukkanin musulmi na duniya da suna rashin amincewarsu da keta alfarmar addinin Musulunci ta hanar kone kur'ani mai tsarki a kasar Amurka.
Ihsan Auglo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, inda ya soki matsayin majalisar kan cin zarafin da musulmi suke fuskanta a kasashan turai.
Ya ce babu wani dalili da zai sanya a kyamaci musulmi da cin zarafinsu, da hana su gudanar da harkokinsu na addini a wata kasa, kamar yadda aka hana su gina masallatai a wasu kasashen turai, ga shi kuma yanzu har ma an kone littafinsu.
656521