Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na risale haber an bayyana cewa, kungiyar kiristoci ta duniya Pax Christi karkashin darikar katolika ta yi kakkausar suka tare da yin allawadai da keta hurumin kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka da kuma nuna kyamar musulmi a kasar Austria.
A cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa babu dalili na daukar karan tsana a dora kan musulmi, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu a wasu kasashen yammacin turai da sunan 'yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi.
Bayanin ya ci gaba da cewa keta alfarmar ur'ani da aka yi ya saba wa koyarwar ddinin kiristanci, kuma kungiyar tana yin Allawadai da hakan, tare da yin kira da aka kawo karshen irin wannan danyen aiki.
656647