IQNA

'Yan Shi'a Jafariyya Sun Yi Allawadai Da Wulakanta Kur'ani

12:09 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996782
Bangaren kasa da kasa; Mabiya mazhabar iayalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya sun yi Allawadai da keta hurumin kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun kiristocin sahyuniya suka a kasar Amurka a cikin wannan wata.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Zainabiyya a birnin Istanbul an habarta cewa, mabiya mazhabar iayalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya sun yi Allawadai da keta hurumin kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun kiristocin sahyuniya suka yi a kasar Amurka a cikin wannan wata da muke ciki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan mutane da suka gudanar da sallar Juma'a a birnin Istanbul sun yi ta rera taken la'antar masu cin zarafin addinin Musulunci, tare da yin Allawadai da keta huumin littafin Allah mai tsarki.

Haka nan kuma wadanda suka gudanar da gangamin nuna goyon baya ga littafin Allah a birnin na Istanbul, sun yi ta la'antar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.

656759




captcha