Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban malamin jami'ar Azhar mai bayar da fatawa a jami'ar ya rushe kwamitin tattuanawa tsakanin addinai wanda jami'ar ta kafa a lokutan da nufin karafa dangantaka tsakaninta da sauran addinai na duniya.
Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa ya rushe kwamitin ne da nufin samar da wata babbar cibiya da za tam aye gurbin wannan kwamitin da zata dauki nauyin gudanar da tattaunawa tsakanin Azhar da sauran cibiyoyin addinai.
Wannan sabuwar cibiya da za a kafa za ta mayar da hankali ne wajen karfafa samun fahimtar juna da girmama akidun kowane addini a duniya, da kuma shiga kafar wandu daya da masu cin zarafin addinai.
658064