IQNA

A Yau Za A Kammala Baje Kolin Kayan Fasahar Musulunci A Glasco

15:07 - September 20, 2010
Lambar Labari: 1997825
Bangaren kasa da kasa; A yau ne za a kammala taron baje koli na kayan fasahar Musulunci a birnin Glasco na kasar Scotland wanda aka fara gudanarwa tun a cikin makon da ya gabata.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islam today an bayyana cewa, a yau ne za a kammala taron baje koli na kayan fasahar Musulunci a birnin Glasco na kasar Scotland wanda aka fara gudanarwa tun a cikin makon day a shige.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen wannan baje koli an kai kayyakin fasaha na Musulunci da dama, da kuma kayyakin tarihi da wasunsu suna komawa zuwa ga karni na goma sha hudu ne wasu kuma karni na sha biyar.

Wasu daga cikin musulmin kasashen turai da suka hada daga kasashen Spain, Girka da kasashen gabacin nahiyar turai da kuma China duk samu halartar wannan baje koli.

657784



captcha