IQNA

An Bude Cibiyar Kur'ani Da Hadisi Ta Zahra (AS) A Pakistan

15:08 - September 20, 2010
Lambar Labari: 1997829
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiyar kur'ani da hadisi Zahra (AS) a birnin Islam bad na kasar Pakistan, tare da halartar makaranci kuma mahardacin kur'ani na kasa da kasa Muhammad Taqi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga reshensa na kasar Pakistan an bayyana cewa, an bude wata cibiyar kur'ani da hadisi Zahra (AS) a birnin Islam bad na kasar Pakistan, tare da halartar makaranci kuma mahardacin kur'ani na kasa da kasa Muhammad Taqi da ke halartar gasa a duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa taron bude wannan cibiya baya ga makaranta daga sassa daban-daban na kasar da suka halarci shi, wasu daga cikin malamai na kasar sun halarci taron deta tare da gabatar da jawabai na fadakarwa.

Babbar manufar wannan cibiya dai ita ce yada ilmomin Musulunci, da kuma kokarin hada kan al'ummar musulmi daga kowane bangare, ta yadda za su iya yin aiki tare da juna domin ci gaba addinin Musulunci.

657842

captcha