Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar zaman ta kasar Turkiya an habarta cewa, Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar Turkiya da zai bahasi kan muhimmancin bunkasa harkokin ci gaban kere-kere a cikin kasashen musulmi musamman a wannan lokaci.
Taron zai mayar da hanakali ne kan bahasi dangane da hanyoyin da za a bi wajen bunkasa harkoki na kere-kere da ci gaban masana'antu a cikin kasashen musulmi, maimakon dogara da wasu kasashe a kowane lokaci.
Majiyar ta ce taron zai samu halartar masana da 'yan kasuwa da masu kamfanoni da manyan masu masana'antiu masu zaman kansu da adadinsu zai hauara mutum dubu uku daga kasashen duniya.
660600