IQNA

15:30 - September 26, 2010
Lambar Labari: 2001761

Malaman Majami'ar Kibtawa Sun Kalubalanci Mai Tozarta Musulunci

Bangaren kasa da kasa; Malaman majami'ar kibtawa a kasar Masar sun yi kakkausar suka kan wani malamin kirista da ya yi furuscin batunci kan kur'ani mai tsarki a kasar, inda suka barranta daga furucinsa.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Almisril yaum an bayyana cewa, malaman majami'ar kibtawa a kasar Masar sun yi kakkausar suka kan wani malamin kirista da ya yi furuscin batunci kan kur'ani mai tsarki a kasar, inda suka barranta daga furucinsa na batunci ga kur'ani mai tsarki.

Babban sakataren cibiyar kiristocin kasar Masar a cikin wani jawabi da ya gabatar ya bayyana cewa a cikin kur'ani mai tsarki an yi karin wasu ayoyi bayan rasuwar manzon Allah (SAW) a lokacin mulkin khalifa na uku, yana kiran musulmi da su cire karin da aka yi cikin kur'ani.

Wannan furuci ya jawo fushin musulmin kasar Masar da ma sauran malaman majami'oin kirista na kasar, inda suke ci gaba da fitar da bayanan yin Allawadai da shi.

662386




captcha