IQNA

Musulmin Italia Sun Bukaci Da A Kawo Karshen Nuna Musu Wariya

15:31 - September 26, 2010
Lambar Labari: 2001765
Bangaren kasa da kasa; Musulmin kasar Italia sun bukaci da a kawo karshen nuna musu wariya da ake yi a kasar a cikin lamurra da dama saboda addininsu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na jaridar kasar masar Al-shuruq cewa, musulmin kasar Italia sun bukaci da a kawo karshen nuna musu wariya da ake yi a kasar a cikin lamurra da dama saboda addininsu a sasas daban-daban na kasar.

Musulmin kasar ta Italia sun koka ne kan yadda mabiya jam'iyar masu tsatsauran ra'ayi na kasar kan takura a cikin dukkanin lamurra, saboda tsananin gabar da wannan jam'iya take yi da addinin Musulunci.

Mabiya addinin muslunci kasar Italia sun bukaci gwamnatin kasar da ta safke nauyin day a rataya kanta na kare rayukansu da dukokiyoyinsu, da kuma mutuncinsu da 'yancinsu.

662240









captcha