IQNA

16:24 - September 28, 2010
Lambar Labari: 2003335

Ministan Ayyukan Na Nwziland Ya Ci Zarafin Musulunci

Bangaren kasa da kasa; Ministan kula da harkokin gine-gine a kasar Newziland Mores Williamsen ya yi wani furuci da a cikin yake cin zarafin musulmi ta hanyar wulakanta akidun muslunci.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Almoslim an bayyana cewa, Ministan kula da harkokin gine-gine a kasar Newziland Mores Williamsen ya yi wani furuci da a cikin yake cin zarafin musulmi ta hanyar wulakanta akidun muslunci, tare da yin zigili.

Ministan wanda daya ne daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Newziland da ke yin da'awar kare hakkin bil adama da demokradiyya ya yi furucin nasa ne wanda ya yi hannun riga da abin suke rayawa.

A cikin 'yan lokutan nan dai kasashen yammacin turai sun tashi haikan wajen yin batunci ga addinin Musulunci da musulmi, inda mutanen gari suka fara, yanzu kuma hart a kai ga mahukunta.

663573



captcha