IQNA

22:50 - October 09, 2010
Lambar Labari: 2009472

Za A Bude Tashar Talabijin Ta Musulunci Ta Farko Da Harshen Italiyanci

Bangaren kasa da kasa, Kungiyar musulmin kasar Italiya na shirin bude wata tashar talabijin ta Musulunci da za ta rika watsa shirye-shiryenta a cikin harshen Italiyanci domin amfanin masu magana da harshen.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na aljazeera an habarta cewa, kungiyar musulmin kasar Italiya na shirin bude wata tashar talabijin ta Musulunci da za ta rika watsa shirye-shiryenta a cikin harshen Italiyanci domin amfanin masu magana da harshen a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tashar talabijin tana daya daga cikin tashoshin talabijin da za su mayar da hankali wajen wayar da kan al'ummomin kasashen turai dangane da addinin muslunci da koyarwarsa.

Musulmin kasar Italia dai su ne marassa rinjaye a kasar, kuma suna gudanar da ayyukansu da harkokinsu na addini a cikin garuruwan da suke da zama, duk da matsalolin da suke samu a wasu lokuta.

670528




captcha