Bangaren kasa da kasa, Musulmin kasar Sweden sun nuna rashin amincewarsu kan shirin nuna wani fim na batunci ga addinin muslunci, wanda jami'ar Absala ta kasar ke shirin gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran muhit an bayyana cewa, Musulmin kasar Sweden sun nuna rashin amincewarsu kan shirin nuna wani fim na batunci ga addinin muslunci, wanda jami'ar Absala ta kasar ke shirin gudanarwa a cikin makon nan.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri nay a kunshi nuna fim din zanen batuncin nan da aka yi kan manzon Allah (SAW) da nufin yiin batunci gare shi da kuma addinin muslunci da musulmi na duniya baki daya.
Yanzu haka dai musulmin kasar ta Sweden suna ci gaba da daukar dukkanin matakan da suka dace domin kalubalantar masu wannan mummunar aniya.
670494