Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa an fara gudanar da taron radiyo da talabijn na kasashen musulmi a yau a babban dakin gudanar da taruka na hukumar radiyo da talabijin din jamhuriyar musulunci ta Iran.
Bayanin ya ci gaba da cewa mahalarta taron sun bayyana cewa dole ne a dauki matakai na bai daya domin tunkarar kafofin yada labaran na kasashe masu nuna matukar adawa da addinin musulunci.
Da dama daga cikin masana da suke halartar taron daga kasashen suniya daban-daban sun goyi bayan daukar matakai na bai daya domin takawa yahudawan sahyuniya birki kan ta'addancinsu.
671992