Bangaren kasa da kasa, Ministan ilimi na kasar Jamus ya yi na'am da furucin da ya fito daga bakin shugaban kasar dangane da hakkin musulmi na zama wani bangare na kasar da suka cancanci kiyaye hakkokinsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Dunya Bulteni an bayyana cewa, ministan ilimi na kasar Jamus ya yi na'am da furucin da ya fito daga bakin shugaban kasar dangane da hakkin musulmi na zama wani bangare na kasar da suka cancanci kiyaye hakkokinsu kamar sauran 'yan kasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar ta Jamus ya bayyana cewa kasantuwar musulmin kasar suna da yawa da ya kai mliyoyi, suna da hakkokin da ya kamata a yi la'akari da su a matsayin wani babban bangare na kasar.
Waziyar kasar Jamus Angela michel wadda take nuna kiyayya ga musulunci ta nuna rashin gamsuwarta da wannan furuci, inda ta tabbatar da cewa addinai biyu kiristanci da yahudanci ne addinan da aka san da zamansu.
673598