Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul Iraq cewa, cibiyar yada koyarwar addinin muslunci ta kasar Holland dake birnin Hague ta shirya nuna wani fim da ke bayyana matsayin kur'ani da mujizar kur'ani.
Rahoton ya ce yanzu haka wannan cibiya ta kammala dukkanin shirinta na nuna wannan fim ga al'ummar kasar Holland da suke bukatar sanin wani abu dangane da addinin muslunci, maimakon dogara da bayanai marassa tushe kan muslunci.
Babbar manufar gudanar da wannan shirin na nuna fim shi ne kara bayar da masani da wayar da kai, da kuma neman samun fahimtar juna tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba.
674229