Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, an fara gudanar da zaman ministocin harkokin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi a birnin Kualalampour na kasar Malazia a jiya Talata.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka taron dai yana samun halartar akasarin ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi da kuma wasu masana daga wasu kasashen wadanda aka aikewa goron gayyata.
Kungiyar bunkasa harkokin ilimi ta kasashen musulmi ISESCI ita ce ta dauki nauyin shirya zaman taron, wanda ke yin dubi kan matsallin ilimi a kasashen musumi da yadda za a bunkasa su.
678299