Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar le monde ta kasar faransa ya watsa rahoton cewa; shugabannin radiyon jama'a a kasar Amerika NPR sun kori Juan Williams fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen wan nan radiyo saboda yadda ya fito karara ya nuna kama kan addinin Musulunci a wani shirin Talbijin. A kwanaki biyu da suka gabata ne Juan a wani shirin talbijin na The O Reilly Facton na gidan Fax ya halarta a lokacin da ke amsa tambayar mai gabatar da shirin kan halin da Amerika ke ciki a yau ya zargi musulmi da rashin bada hadin kan don warware wannan halin tsaka mia wuya da Amerika ke ciki. Wannan dangatawa day a yin a nuni kara da yadda yake adawa da musulmi da Musulunci.
679906