IQNA

An Nuna Kayayyakin Fasahar Mata Musulmi Na Thailand Kan Kur'ani

12:40 - October 26, 2010
Lambar Labari: 2019665
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani taro da aka nuna wasu daga cikin kayan fasaha da wata mata musulmi 'yan kasar Thailand ta yi da hannuta, da suke da dangantaka da kur'ani mai tsarki da kuma addinin muslunci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na sunu an bayyana cewa, a gudanar da wani taro da aka nuna wasu daga cikin kayan fasaha da wata mata musulmi 'yan kasar Thailand ta yi da hannuta, da suke da dangantaka da kur'ani mai tsarki da kuma addinin muslunci da tasirinsa a tsakanin al'ummar kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mata ta taka gagarumar rawa wajen bayyana hakikanin koyarwa ta addinin muslunci a tsakanin al'ummar kasar ta hanyar zane-zane, da kuma samar da wasu abubuwa na fasaha da ke nuni da hakan a cikin hikima.

Yanzu haka dai dubban musulmi daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashe na ketare suke halartar taron nuna kayan fasar da samar da suke nuna matsayin addinin Musulunci da sahihiyar koyarwa a tsakanin al'ummomin duniya.

681585






captcha