Bangaren kasa da kasa; a karo na uku taron yankin na kungiyoyin duniya kan sulhu a Musulunci da aka bawa taken sulhu kan adalci da tattaunawa ta bai daya a duniya da aka gudanar a ranekun shida da bakwai ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Atava fadar mulkin kasar Kanada inda aka samu wakilai daga kasashen Amerika,Kanada,Venuzuwela da jamhuriyar Musulunci ta Iran.