Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar Masar tare da hada baki da majiyoyin tsaro na kasar kimanin kur'aniai dubu hudu ne da aka rage wasu ayoyi a cikin wasu surori da kuma ke cike da kurakurai na nahauwin larabci da larabcin kansa aka aike zuwa wajen kasar. Daga cikin surorui da ayoyin da aka fitar da su daga cikin jerin ayoyin kur'ani akwai wasu magana kan jihadi da sha giya da tarihin kissoshin bani Isra'ila da Annabi Musa (AS).
701681