Banagren kasa da kasa; Imam Musa Sadre a cikin wasu ayoyi da surori na kur'ani musamman suratul Takasur ya yi amfani da hudubobin Hadarat Ali (AS) da ke cikin littafin Nahajul balaga.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Imam Musa Sadre a cikin wasu ayoyi da surori na kur'ani musamman suratul Takasur ya yi amfani da hudubobin Hadarat Ali (AS) da ke cikin littafin Nahajul balaga. Majid Ma'arif mamba a tawagar malaman karamar jami'a ta koyar da ilimin sanin Allah da addinin Musulunci a jami'ar Tehran kuma mamba a hadin guiwar malama masu nazari kan ilimin kur'ani da hadisai a Iran a wani zaman binciken nazari kan tafsirin kur'ani na Imam Musa Sadre ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Ikna da cewa; idan suna so mu fahimci abubuwan da imam Musa Sadre ya tasirantu da su a cikin tafsirinsa to za mug a cewa ya amfani ne da kur'ani da hadisai da kuma hudubobi da bayanai na A'ima (AS)
707778