IQNA

10:18 - December 20, 2010
Lambar Labari: 2050103

Allamah Balaghi Na Ganin Yin Amfani Da Hankali Na Muhimmanci A Tattaunawar Addinai

Bangaren kasa da kasa, Allamah Balaghi wanda daya daga cikin manayan malaman addinin muslunci na ganin cewa yin amfani da hanakali na daya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata amayar da hankali kansu a lokacin tattaunawa tsakanin mabiya addinai.




A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da wani mai yin nazari kan addinin muslunci Muhammad Ali Mohammadi ya bayyana cewa, Allamah Balaghi wanda daya daga cikin manayan malaman addinin muslunci na ganin cewa yin amfani da hanakali na daya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata amayar da hankali kansu a lokacin tattaunawa tsakanin mabiya addinai da aka safkar daga sama.

Ya ci gaba da cewa akwai babban abin lura a cikin mahangar ta Allamah Balaghi, domin kuwa dukkanin addinai suna da abin da suka yi imani da shi na daga littfansu, da kuma koyarwar da ke ciki, a kan haka kafa dalili da mahanga ta imani da addini ba zai iya kawo fahimtar juna ga baki daya ba.

Malamin ya ce tattaunawa tsakanin addinai na da matukar muhimmanci, domin kuwa ta hakan ne kawai za a iya warware da dama daga cikin matsalaoli da rshin fahimta da ke akwai tsakanin mabiya addinai.

714406


captcha