IQNA

16:00 - December 22, 2010
Lambar Labari: 2051857

Za A Fara Rijistar Sunayen Masu Halartar Horon Karatun Kur'ani A Niger

Bangaren kasa kasa, A gobe idan Allah ya kai mu ne za a fara gudanar da rijistar sunayen masu bukatar shiga shirin nan na horoar da masu koyon karatun kur'ani mai tsarki a birnin Yamai na jamhuriyar Niger.




Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na actualite-islaque cewa, agobe idan Allah ya kai mu ne za a fara gudanar da rijistar sunayen masu bukatar shiga shirin nan na horoar da masu koyon karatun kur'ani mai tsarki a birnin Yamai na jamhuriyar Niger a ginin babbar cibiyar kula da bunkasa ayyukan musulunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan rijista za a ci gaba da gudanar da ita har zuwa ranar Talata ta makon gobe, domin bayar da dama ga masu bukata su je su yi rijistar sunayensu, kuma za a bayanna lokacin fara gudanar da shirin bayar da horon da zaran an kammala yin rijistar suyen.

Jamhuriyar na daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka da ke bayar da muhimmanci wajen koyar da karatun kur'ani, kamar yadda kasar mamba akungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya.

716046


captcha