Ana Shirin Gudanar Da Zaman Kwamitin Kungiyoyin Musulmi A Switzerland
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin wakilan kungiyoyin musulmi na kasar Switzerland na shirin fara gudanar da zamansa na shekara-shekara da ya saba gudanarwa tare da halartar wakilan wasu kungiyoyin da ke cikin kasashen turai.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da samu daga jaridar Al-watan ta kasar Saudiyya an habarta cewa, kwamitin wakilan kungiyoyin musulmi na kasar Switzerland na shirin fara gudanar da zamansa na shekara-shekara da ya saba gudanarwa tare da halartar wakilan wasu kungiyoyin da ke cikin kasashen turai da sauran kasashen musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro shi ne karo na talatin da kwamitin zai gudanar, wanda kuma zai bahasi ne kan muhimman batutuwa da suka fanganci yanayin rayuwar musulmi ta zamantakewa musamman a cikin kasashen yammacin turai.
Kwamitin wakilan kungiyoyin musulmi na kasar Switzerland na shirin fara gudanar da zamansa na shekara-shekara da ya saba gudanarwa tare da halartar wakilan wasu kungiyoyin da ke cikin kasashen turai da ketare.
717438