IQNA

15:20 - December 28, 2010
Lambar Labari: 2054990

Masu Tsananin Ra'ayin Addini Suna Yi Wa Yan Uwa Musulmi Barazana

Bangaren kasa da kasa:Malamai da manazarta da suka halarci taron kasa da kasa na Aljeriya sun jaddada cewa masu tsananin ra'ayin addini bayan suna wargaza zaman tae sun kuma yin barazana wa hadin kai day an uwan taka a tsakanin al'ummar musulmi.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta alwatan ya watsa rahoton cewa; Malamai da manazarta da suka halarci taron kasa da kasa na Aljeriya sun jaddada cewa masu tsananin ra'ayin addini bayan suna wargaza zaman tae sun kuma yin barazana wa hadin kai day an uwan taka a tsakanin al'ummar musulmi.Har ila yau mahalarta taron sun jaddada da babbar murya kan bin hanyoyin da suka dace cikin sauki na warwarewa da magance matsalolin da ke addabar duniyar musulmi da kuma yakar wannan matsala ta tsananin nuna ra'ayin addini a cikin kasashen musulmi. Kuma wasu sun yi bayani kan yadda za a magance wannan matsa ta hanyar tunani da yin nazari na ilimi da bayanai masu gamsarwa.


718963
captcha