IQNA

Masu Tsatsauran Ra'ayi Ba Za Su Iya Kawo Baraka Tsakanin Al'umma Ba

17:44 - January 04, 2011
Lambar Labari: 2058988
Bangaren kasa da kasa, Daya daga cikin malaman Masar ya ce za a kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin mabiya addinin kirista da kuma mabiya addinin Musulunci a kasar Masar da nufin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinan biyu na kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, za a kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin mabiya addinin kirista da kuma mabiya addinin Musulunci a kasar Masar da nufin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinan biyu da ke zaune.

Rahoton ya kara da cewa babbar manufar kafa wanna kwamiti ita ce haifar da yanayi na zaman lafiya da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula tsakanin mabiya addinan biyu, musamman ma a cikin 'yan lokutanan, lamarin da ya fuskanci Allawadai daga malaman addinin muslunci da kungiyoyi.

A cikin watan decemban da ya gabata an kai wasu hare-hare kan majami'oin mabiya addinin kirista a Masar, kamar yadda aka kai wasu makamantansu a lokacin da suke bukin sabuwar shekarar bana ta 2011.

723221



captcha