IQNA

A Shekara Mai Zuwa Za a Bude Babban Bankin Musulunci A Kasar Qazakistan

14:08 - January 05, 2011
Lambar Labari: 2059549
Bangaren kasa da kasa, A cikin shekara mai zuwa ne za a bude babban bankin muslunci na biyu a kasar Qazakistan, wanda zai kula da wasu daga cikin harkokin kudade da cinikayyar musulmi da suke bukatar gudanar da harkokinsu bisa kaidoji da dokokin addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, a cikin shekara mai zuwa ne za a bude babban bankin muslunci na biyu a kasar Qazakistan, wanda zai kula da wasu daga cikin harkokin kudade da cinikayyar musulmi da suke bukatar gudanar da harkokinsu bisa kaidoji da dokokin addinin muslunci da suka yi imani da su.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shirye na bude wannan banki, amma bisa ga ka’ida za a gudanar da taron budewar ne a hukumance a cikin a cikin shekara ta 2012, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da kuma ‘yan kasuwa musulmi na kasar da ma wadanda ba musulmi ba, gami da wakilan cibiyoyin kudade da kasuwanci na wasu kasashen musulmi.

A shekara mai zuwa ne ta 2012 za a bude babban bankin muslunci na biyu a kasar Qazakistan, wanda zai kula da wasu daga cikin harkokin kudade da cinikayyar musulmi da suke bukatar gudanar da harkokinsu bisa kaidoji da dokokin addinin muslunci da kuma koyarwarsa.

724101


captcha