Bangaren kasa da kasa; Ali Akbar Salihu mai kula da ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran a ranar sha shidda ga wata Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin day a ke ganawa da Ayatullahi uzma Said Ali Sistani a birnin najaf ya gabatar da wannan babban malamin marji'in yan shi'a a matsayin babbar madogara mai muhimmanci ta samar da hadin kai da magance sabani a tsakanin Irakiyawa.