IQNA

10:21 - January 13, 2011
Lambar Labari: 2063851

Kin Amincewa Da Daftarin Hana Saka Hijabin Musulunci A Albania

Bangaren kasa da kasa, An ki amincewa da wani daftarin doka da ke neman hana saka hijabin muslunci a makarantun kasar Albania, wanda aka gabatarwa majalisar dokokin kasar da nufin ta amince da shi domin ya zama doka a cikin tsarin mulkin kasar.


Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na la-croix an bayyana cewa, daya daga cikin shugabannin jami'ar Musulunci ta kasar Albania Haji Salim Musa ya bayyana cewa, ba za su taba amincewa da wannan mataki da ake neman dauka a kan musulmin kasar ta Albania ba.

Ya ce babbar manufar hakan ita ce kawar da duk wata koyarwar Musulunci a tsakanin al'ummar kasar, wadanda suke da dadden tarihin rungumar addinin muslunci, ya jaddda cewa, saka hijabi daya ne daga cikin abubuwan da suka rataya kan musulmi a addininsa, saboda haka babu dalilin hana shi aiwatar da koyarawa addininsu.

Kin amincewa da daftarin doka da ke neman hana saka hijabin muslunci a makarantun kasar Albania, wanda aka gabatarwa majalisar dokokin kasar da nufin ta amince da shi domin ya zama doka a cikin tsarin mulkin kasar, ya nuna tsayin dakan musulmin kasar ne.

729284




captcha