Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Qatar ta Al-sharq an bayyana cewa, an zabi Abdullah Bisfar babban sakataren kwamitin hardar kur’ani na duniya a matsayin gwarzon shekara ta 2010 na kasashen larabawa ta fsukar gudanar da kwazo a bangarorin da suka danganci yada lamarin kur’ani a cikin sassa na duniya, wanda kwamitin zaben gwarazan kur’ani na kasashen larabawa ya sanar a birnin Doha na kasar.
A cikin bayanin da kwamitin zabar gwarazan kur’ani na kasashen larabawa ya fitar ya bayyana cewa, wannan dan taliki ya taka gagarumar rawa a fagage daban-daban, kama daga cikin kasashen larabawa da na musulmi har zuwa wasu kasashen sauran nahiyiyon duniya domin isar da lamarin kur’ani, wanda hakan a ganin kwamitin ya cancancin wannan lambar yabo.
Zaben Abdullah Bisfar babban sakataren kwamitin hardar kur’ani na duniya a matsayin gwarzon shekara ta 2010 na kasashen larabawa ta fsukar gudanar da kwazo a bangarorin da suka danganci yada lamarin kur’ani a cikin sassa na duniya, wanda kwamitin zaben gwarazan kur’ani na kasashen larabawa ya sanar a birnin Doha na kasar Qatar, babban ci gaba ne ga harkar kura’ni.
730124