Bangaren kasa da kasa, Wasu 'yan kasar China da ke yin aiki tare da wani kamfanin kasar a kasar Iraki, suna bayar da ruwan sha ga dubban daruruwan Irakawa masu ziyarar Imam Hussain a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan cika kwanaki arba'in da wucewar ranar Ashura.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, wasu 'yan kasar China da ke yin aiki tare da wani kamfanin kasar a kasar Iraki, suna bayar da ruwan sha ga dubban daruruwan Irakawa masu ziyarar Imam Hussain a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan cika kwanaki arba'in da wucewar ranar Ashura da aka saba gudanarwa a kowace shekara a hubbarensa mai tsarki.
Tarukan tunawa da ranar arba'in na daga cikin ranaku masu albarka da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suke gudanarwa a kowace shekara, inda sukan halarci tarukan daga cikin gida da kuma kasashen duniya daban-daban, domin raya lamarin iyalan gidan manzon Allah (SAW) musamman ma shahadar Imam Hussain (AS)
'Yan kasar China guda biyu mata da miji, suna raba abinci da kayan marmari ga masu ziyarar Imam Hussain (AS) inda kuma su ma suke cikin masu tafiya zuwa hubbaren nasa mai alfarma domin halartar wadannan taruka masu albarka da za a gudanar.
Mutanen biyu da ke yin aiki tare da wani kamfanin kasar a kasar Iraki, suna bayar da ruwan sha ga dubban daruruwan Irakawa masu ziyarar Imam Hussain a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan cika kwanaki arba'in da wucewar ranar Ashura.
732792