Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Altahira an bayyana cewa, Kwamitin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Tunisia ya fitar da wani bayani dangane da halain da ake ciki a kasar bayan faduwar daular tsohon shugaban kasar Zainul abiding bin Ali, wanda ya gudu zuwa kasar Saudiyya a matsayin dan gudun hijira a kasar.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Tunisia sun jima suna fuskantar matsaloli daga tsohon shugaban kama karya karyan kasar Tunisia Zainul abiding, wanda yake samun cikakken goyon baya daga kasashen yammacin turai musamman ma Amurka da Faranda da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila.
Wannan kwamiti na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Tunisia da ya fitar da bayani dangane da halain da suke ciki a kasar bayan faduwar daular tsohon shugaban kasar Zainul abiding bin Ali, ya jaddada wajabcin yin tsayin daka domin baiwa kowa hakkokinsa a matsayin dan kasa.
732732